YAKIN ISRA’ILA DA GAZA: Kasashen Duniya Na Fargabar Cewa Babu Wata Hanyar Da Fararen Hula Za Su Iya Gujewa Rikicin

Palestinians inspect the site of Israeli strikes in Khan Younis

Dakarun Isra’ila sun fafata da mayakan Hamas a zirrin Gaza, jiya Talata inda suka fi mai da hankali a kudancin Gaza, yayin da kugiyoyin jinkai da kasashen duniya su ke bayyana fargabar cewa babu wata hanyar da fararen hula zasu iya guje wa rikicin. 

Tankoki yakin Isra’ila da dakarunta sun kutsa kusa da Khan Younis, birni na biyu a grima a Gaza, yayin da hare-haren saman Isara’ila suke auna kudancin Gaza. A ‘yan kwanakin bayan nan, Isra’ila ta yi wa mutane gargadi domin su samu damar ficewa daga unguwannin Khan Younis da dama domin kare kansu inda ta umarce su da su tafi can sashin kudu.

Mutane da dama sun gudu daga arewacin Gaza zuwa kudancinta a farkon rikicin yayin da Isra’ila ta kaddamar da kai wa Hamas hari a yankunan birnin Gaza.

Gaza

Jakadan MDD mai tsara ayyukan jinkai a yankin Filasdinu da aka mamaye, Lynn Hastings, ya fada cikin wata sanarwa a ranar Litinin cewa “babu inda yake da tsaro, kuma babu inda ya rage da mutane zasu iya zuwa.

Isra’ila ta kaddamar da hare-haren soji da zummar kawo karshen mulkin Hamas a Gaza bayan da mayakan Hamas suka tsallaka cikin kudancin Isra’ila a ranmar 7 ga watan Oktoba. Isra’ila ta ce an kashe mutum 1,200 sannan kuma an yi garkuwa da wasu 240.

Tuni dai aka yi musayar kimanin mutanen da ake garkuwa da su 100 da fursunoni ‘yan Filasdinu 100 wadanda Isra’ila ta ke tsare da su.

Akalla mutum 15,890 ne aka kashe a Gaza, kuma kashi 70% cikin su yara da mata ne, a cewar ma’aikatar lafiyar Gaza wadda ke karkashin Hamas.