Mahalarta taron na ganin akwai kalubale da matsaloli dake yin tarnaki ga kokarin kawar da cin hanci da rashawa wadanda kuma suke neman gurgunta tattalin arzikin kasar.
Shugaban hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Muibi Magajin Rimin Gado ya gabatar da kasida akan kalubalen yaki da cin hanci da rashawa.
Yace kalubalen kuwa sun hada da barin gwamnatin tarayya ita kadai da fafutikar. Yace irin tasu hukumar nawa ne a sauran jihohin. Bisa ga tsarin mulkin kasar hatta kananan hukumomi yakamata suna da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa amma ba haka lamarin yake ba.
Ya bada misali da hukumar EFCC wadda babu ita a Sokoto da Kebbi. Idan wani abu ya faru saidai an je Kano domin ofishin dake Kano ne yake kula da arewa maso yammacin kasar. Amma idan jihohi nada nasu hukumomin zasu taka tasu rawar wajen yakar cin hanci da rashawa.
Baicin yadda mutane ke son kare wadanda aka zarga da cin hanci da rashawa wasu dokokin kasar na kawo cikas da yaki da mummunan dabi'ar inji Muibi Magaji. Da an tsaurara dokokin da watakila su tsorata mutane da yin aika aikar.
Ga rahoton Murta Faruk Sanyinna da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5