Ranar 15 ga watan Disambar bara ne gwamnatin jihar Legas ta bayyana fara sayar da kilogram hamsin na shinkafa akan N13,000 yayinda ta ce zata sayar da kilogram 25 kan N6, 000 ga al'ummar jihar.
Mai ba gwamna Akinwumi Ambode shawara akan harkokin abinci Mr. Sani Okanlawon shi ya bada sanarwar. Yace tsarin na gwamnati an bullo dashi ne sakamakon wani shiri na hadin gwuiwa da jihar ta cimma da jihar Kebbi inda shinkafar ta fito da aka sa mata suna Lake Rice.
Gwamnatin ta shirya ta sayar da shinkafar ne a kananan hukumomi hamsin da bakwai na jihar domin rage tsadar farashin shinkafa.
To saidai binciken da aka gudanar a yankunan da gwamnatin ta bada sanarwar za'a sayar da shinkafar an samu karancinta. Wadanda aka zanta dasu sunce basu samu sun saya ba. Amma wasu kalilan sun samu.
To saidai wani jami'in gwamnatin Legas yace ana sayarda shinkafar ne a hedkwatar kananan hukumomi da wasu cibiyoyi da gwamnati ta kebe ba a kasuwa ba kamar yadda wasu suka yi zato.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.