Kamar yadda aka sani, yaki da cin hanci da rashawa na cikin batutuwan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin aiwatarwa tun lokacin da yake yakin neman zabe. Kuma 'Yan Najeriya da dama na ganin babu mutumin da ya cancanci ya aiwatar da wannan shiri kamar sa musamman idan aka yi la'akari da dattakunsa da kuma tarihinsa na kyamar cin hanci.
A baya bayan nan ne shugaba Buhari ya dakatar da sakataren Gwamnatin sa Mr Babachur David Lawal da kuma shugaban hukumar leken asirin kasar, NIA, bisa zargin laifukan cin hanci da rashawa, wanda kuma nan take shugaba Buhari ya nada mataimakinsa Osinbajo da ya jagoranci gudanar da bincike game da laifin da ke kan Babachir Lawal da shugaban hukumar ta NIA.
To sai dai kuma, yayin da ake fara wannan bincike har yanzu ‘yan Najeriya na ganin akwai wasu jami’an gwamnatinsa da dama da ake zargin na cin hanci cikinsu har da, wanda ake zargi da mallakar manyan gidaje na sama da Dala Miliyan ‘daya da rabi a birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa. Haka nan kuma, ga batun badakalar MTN, lamarin da yanzu haka yan kasar ke tsokaci.
Masu sharhi na ganin lokaci ya yi da shugaba Buhari zai dauki matakin ba sani ba sabo, a yakin da yake yi da cin hanci idan ba haka ba zai faɗi ba nauyi kamar yadda Hussaini Bello Gambo na Kura wani dan fafutuka a Najeriya, yace akwai abin dubawa.
Shi ma wani masani a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Adamawa, wato SPY, Abdulmumini Ibrahim Song, yace ko ba komi shugaba Buhari ya cancanci a yaba masa.
To sai dai kuma ga yan siyasa irinsu Abdullahi Prembe, ‘kusa a jam’iyar PDP, na mai ra’ayin cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta fara sanya shakku a zukatan 'yan kasar game da aniyarta ta yaki da cin hanci da rashawa.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5