Shehun Bornon yayi kiran ne lokacin da kungiyar bada agaji ta al'ummar Musulmai dake kasar Saudiya ta kawo tallafi ga wasu 'yan gudun hijirar dake jihar.
Wanda ya wakilci Shehun yace akwai bukatar irin taimakon da aka kawo a kananan hukumomi ganin irin halin da al'ummar jihar suka shiga.
Shehun Borno yayi matukar farin ciki da taimakon da aka kawowa al'ummarsa kana ya kara da rokon kungiyar ta zabi koda kananan hukumomi uku ta kai irin wannan tallafin..
Abdal Huseini Abdalla daraktan kungiyar ya lissafa abubuwan da suka zo dasu domin taimako tare da ambatar sansanonin da zasu ziyarta saboda raba kayan agajin.
Baicin kayan da suka kawo kungiyar tana da marayu sama da dari shida da take kula dasu ta hanyar ciyar dasu da biyan kudin makarantun da suke zuwa.
Wadanda suka sami taimakon da ya lakume Naira miliyan talatin da shida sun nuna godiyarsu.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Facebook Forum