Yajin Aikin Wasu Likitoci A Jihar Osun

Kwararren likita yana bincike kan kwayar cutar Malaeriya a wani asibitin kasar Kenya a watan Nuwambar 2010.

Wasu likitoci a jihar Osun, sun kwashe watanni masu yawa suna yajin aiki a bisa rashin isassun kayan aiki kamar gadajen kwanciyar majinyata da magani da wasu ababen aiki da suke bukata don gudanar da ayyukansu.

Kan wannan batu ne wakilin Muryar Amurka Hassan Tambuwal, ya kira babban likita mai magana da yawun gwamnatin jihar Osun ta wayar tarho Farfesa Hakeem Lasisi, wanda yace akwai likitoci kimanin 33 a cikin 180 zuwa 200 na asibitin koyarwa dake wanda ke yajin aikin wadanda suka share shekaru 6 suna koyan aiki, wanda hakan ka’ida ne a fadin Duniya, bayan kammala aikinsu suka ki tafiya. Kuma wannan shine dalilin yajin aikin nasu inji Farfesa Hakeem.

Farfesa Hakeem, ya musanta maganar cewa babu kayan aiki a asibiti domin likitoci 33 da ukune kadai ke wannan yajin aikin, ya kumace me yasa sauran likitocin basa yajin aikin.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Yajin Aikin Wasu Likitoci A Jihar Osun - 3'26"