Wannan tashin bom din ya farune a dai dai lokacin da ake tantance ma’aikata a sakatariyar, wanda kuma ya kasance karo na farko da aka sami irin wannan tashin bon a wannan ma’aikata. Tuni dai gwamnan jihar Borno da sauran jami’an tsaro suka ziyarci wannan wuri, haka kuma sun ziyarci asibitin da aka kwantar da mutanen da suka sami raunuka.
Rahotanni dai na cewa bom din ya tashi a dai dai inda jami’an yan Sanda ke bincikar ababawan hawa dab da shiga sakatariya. Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda, ya tuntubi kwamishinan yan sandan jihar don neman karin bayani, sai dai kwamishinan bashi da hurumin yin magana domin yana cikin wani taro.
A jiya ne rundunar sojan Najeriya, ta fitar da wata sanarwa dake cewa ta kawar da yiwuwar kunar bakin wake a unguwar Silimanti da wani yayi kokarin shigowa da shi.
Domin karin bayani.