Taron ya gudana ne a birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno a karkashin jagorancin addinan musulunci da kiristanci.
Shugabannin Imam Dr. Nuren Ashafa da Pastor James Wuye sun gabatar da laccoci ga matan musamman wadanda aka kashe mazajensu.
Kungiyar ta zabi zuwa birnin Maiduguri ne ganin cewa irin mutane da suka samu dimuwa sun fi yawa a jihar Borno kuma ta wannan yanya ce kungiyar zata iya bada tata gudummawar.
Pastor James Wuye ya yi bayani akan yadda zasu taimakawa matan. Yace sun zo ne su taimaka masu ta yin anfani da kwakwalwarsu domin su shiga cikin hankalinsu. Idan mutum ya shiga cikin hankalinsa to duk wani taimako da aka yi masa zai anfana. Amma idan mutum baya cikin hankalinsa komenene aka kawo masa zai yi watsi dashi.
Shi ma Imam Nuren Ashafa ya bayyana dalilansu na bada gudummawar. Yace a cikin masifar da kasar ta samu kanta wadanda abun ya fi shafa da yawa su ne iyaye mata musamman wadanda suka rasa gidajensu da mazajensu da kuma 'ya'yansu. Tunda gwamnatin tarayya ta dauki nauyin gyara masu muhallansu da kula da abun da zasu ci, amma babu wanda ya kula da ruhaniyarsu saboda haka ne kungiyarsu ta fito ta yi taimako.
Su ma matan da aka horas sun fadi albarkacin bakinsu. Sun ce sun gode tare da 'ya'yansu bisa ga horon da suka samu.
Ga karin bayani.