Yajin Aiki Ba Gudu Ba Ja Da Baya: ASUU

Dalibai Masu zanga zanga a Jami'ar Calabar 12, ga Oktoba 2015.

Kungiyar malaman jami’o’i ta yi watsi da umarnin gwamnatin tarayyar Najeriya da ta bukace su su koma bakin aiki a ranar 12 ga watan Oktoba.

Kungiyar malaman jami’o’in-ASUU ta bayyana cewa za su ci gaba da yajin aikin sakamakon rashin biyan bukatun malamai a fanni albashi da alawus-alawus.

Kusan duk shekara malaman jami’o’in Najeriya na yajin aikin gamagari domin nuna rashin jin dadin su a kan yadda gwamnati ke barin gibi a lamurran ilimi da malamai da kuma mika bukatun a rinka biyan hakokkin su a kan lokaci, sai dai yawancin lokuta gwamnati ta kan yi alkawarin biyan bukatun amma daga baya a samu sabani da ke tilastawa malaman komawa gidan jiya, sakamakon rashin mutunta yarjejeniya da aka cimma lamarin da ke sa malaman daukar matakan tsunduma cikin yajin aiki.

daliban-jami-oi-sun-koka-kan-yajin-aikin-malamai

kungiyar-manyan-maaikatan-jamioi-na-zanga-zangar-lumana-a-najeriya

najeriya-asuu-ta-janye-yajin-aiki

Shugaban kungiyar malaman jami’o’i, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta da gaskiya a kan tattaunawar da ta ke da kungiyar, ya na mai cewa, malamai ba zasu koma bakin aiki da yunwa ba.

Bukin yaye daliban Jami'a a Najeriya

Ogunyemi dai ya caccaki akanta janar na Najeriya, Mallam Ahmad Idris, sakamakon sabawa umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar na a biya malamai albashin su yana mai cewa ‘yan kasar su shiryawa gagarumin yajin aikin da jami’o’i zasu shiga saboda yadda gwamnati ke wasa da tattaunawar su.

Kazalika, kungiyar ma’aikatan jami’o’i wadanda ba sa koyarwa ma ta yi korafi a kan tsarin biyan albashi na bai daya wato IPPIS da ba a aiki a bayyane ta na mai cewa ana cutar da yawancin mambobinta da tsarin.

Idan ba a manta ba, kafin rufe makarantu a watan maris sakamakon annobar Coronavirus, akwai rashin jituwa tsakanin gwamnatin tarayyar kasar da kungiyar ASUU a kan tsarin biyan albashi na bai daya wato IPPIS inda ta ce gwamnati ba zata aiwatar da tsarin ba saboda hakan zai sabawa yancin kungiyar.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra’uf cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Yajin Aiki Ba Gudu Ba Ja Da Baya: ASUU-3:00"