Tun a cikin shekara ta 2009 ne kungiyar malaman Jami’a ta ASUU ta kulla wata yarjejeniya da gwamnatin tarayyar Najeriya, game da wasu batutuwa da suka shafi walwalar malaman Jami’o’i da inganta kayan koyo da koyarwa ga dalibai, da kuma kyautata ayyukan bincike a Jami’a.
A shekara ta 2014 kungiyar malaman tayi wani dogon yajin aiki saboda abin da ta kira rashin mutunta wancan yarjejeniyar daga bangaren gwamnati. Sai dai kuma kungiyar ASUU bata gamsu da yadda gwamnatin Najeriya ke aiwatar da waccan yarjejeniya ba, domin kuwa jiya Laraba ne ta umarci ‘ya ‘yanta da su tafi yajin aikin gargadi na tsawo mako daya.
Wasu dalibai a jihar Kano sun bayyana rashin jin dadinsu ga wannan yajin aiki, kasancewar zai shafi karatunsu matuka, ya yin da wasu daliban ke cewa yanzu haka ya kamata su fara rubuta jarabawa sai gashi an fara yajin aiki.
Sai dai masu fashin baki na ganin ya kamata gwamnatin tarayya ta sake salon yadda take tafiyar da ayyukan ilimin Jami’o’i, domin kawo karshe matsaloli ga ‘ya ‘yan talakawa dake karatu suke samu. Su kuma malaman jami’a su ringa la’akari ga rayuwar dalibai, a cewar mallam Bashir Mohammad Bashir, mai sharshi kan al’amuran yau da kullm.
Yanzu haka dai rahotanni na cewa shugabancin Majlisar Dokoki ya gayyaci magabatan kungiyar malaman Jami’o’in domin tattaunawa kan wannan al’amari.
Domin karin bayani.