Kungiyar wadda ke bibiyar abubuwan da ke faruwa a Arewacin Najeriya ta kira dukkan kungiyoyin yankin ne don fitar da tsarin ceto arewa daga halin da ta ke ciki yanzu.
Shugaban Cibiyar yada kyakkyawar fahimta tsakanin mabiya addinai a Najeriya, Imam Muhammad Nurain Ashafa, ya ce komawa kan tafarkin hadin kai ne maganin matsalolin arewa.
Imam Ashafa ya ce matukar mabiya addinai da kabilu ba su hada kansu ba, to Najeriya ba za ta taba ci gaba ba.
Shi kuwa shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin arewa, Alhaji Nastura Ashir Sherif, cewa ya yi matsalolin yankin sun taso ne daga rashin shugabanci na gari.
Sheriff ya ce akwai bukatar samar da shugabanni masu tsoron Allah don kawo ci gaban da ake bukata a Najeriya.
Alhaji Ibrahim Abdullahi, shi ne babban sakataren kungiyar Fulani ta Gam-Allah, ya ce idan aka magance matsalolin yankin arewa, to Najeriya za ta samu tsira baki daya.
Kungiyoyi da dama ne su ka halarci wannan taro wanda ya tashi da matsayar magance rarrabuwar kan al'umomin yankin arewa baki daya.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5