Dan takarar jam’iyyar PNDS TARAYYA mai mulki Issoufou Mahamadou, na daga cikin wadanda suka kammala yakin neman zaben da taron gangami jiya Juma’a a birnin Yamai. Saboda haka magoya bayan shugaban suka hallara a wani filin kwallon kafa domin cashew da kade kade.
Daba baya Issoufou Mahamadou, neman wa’adin mulki na biyu a fafatawar da zaiyi da ‘yan takara kimanin 14, ya kara jaddada burin lashe zaben na ranar Lahadi 21 ga wannan watan tun a zagayen farko.
Itama babbar jam’iyyar adawa ta MNSD NASSARA wadda ‘dan takarar ta Seyni Oumarou, ya rufe nasa gangamin jiya Juma’a a birnin Maradi, inda yake cewa babu makawa wannan zabe zaije zagaye na biyu.
Yayin da ‘dan takarar Jam’iyyar MPN KISHIN KASSA, Ibrahim Yacouba, ya shirya gangamin kammala kamfen a babban filin kwallon kafa na Yamai. Rahotanni sunce ‘dan takarar MNRD HANKOURI, Mahamane Ousmane ya kammala nashi ne a Damagaram.
Haka suma sauran ‘yan takarar sun kammala nasu ne a can jahohin da zasu yi zabe, yakiin zaben na bana na zuwa karshe ne alokacin da ‘yan adawa suka bada sanarwar shigar da karan hukumar zabe ta CENI gaban kotun tsarin mulkin kasa, bisa zarginta da taka doka saboda yin zabe ta hanyar gabatar da shedu a maimakon katin dan kasa.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5