Yayin da saura kwanaki kadan suka rage a fara azumin watan Ramadan a bana, dubban 'yan gudun hijirar dake tattare a sansanoni dabam-dabam da aka ajiye su ciki a Jihar Adamawa, sun koka game da halin da suke ciki tare da neman a kai musu agaji.
Wani dan gudun hijira mai suna Sulaiman daga Gwoza a Jihar Borno, yayi rokon da hukumomi da jama'a su taimaka musu ta yadda zasu yi azumi kamar kowa da kowa.
Wata 'yar gudun hijirar mai suna Jummai daga garin Madagali na Jihar Adamawa kuma, ta ce su na cikin mawuyacin hali na wata da watanni, don haka suke rokon a taimaka musu da kayan azumi, a kuma kokarta mayar da su garuruwansu saboda damina tazo.
Alhaji Sa'adu Bello, babban jami'in hukumar agajin gaggawa ta kasa a Jihar Adamawa, yace hukumarsa ta NEMA ta yi tanadin samarwa da 'yan gudun hijirar abinci na sahur da bude baki a kullum, a duk tsawon azumin.
Ya roki jama'a masu hannu da shuni da su tallafa da duk irin agajin da zasu iya.
Your browser doesn’t support HTML5