Akalla mutum takwas rahotanni suka ce ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su a wani asibitin gwamnatin tarayya da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a asibitin da ake kula da masu lalurar tarin fuka da ta kuturta da ke Zaria da misalin karfe 1:30 na tsakar daren ranar Lahadi.
Bayanai sun yi nuni da cewa ‘yan bindigar har ila yau sun kai hari wani ofishin ‘yan sanda da ke yankin.
Wasu rahotannin sun ce mutum bakwai aka sace ciki da har da ma’aikatan jinya da jarirai kamar yadda jaridun Najeriya da dama suka ruwaito.
Yankin garin Zaria a ‘yan kwanakin nan yana yawan fadawa tarkon ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
A watan da ya gabata wasu ‘yan bindiga suka far wa kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli inda suka yi awon gaba da dalibai da malamai.
Yawan hare-haren har ya sa masarautar Zaria ta yi kira ga hukumomi da su tashe tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin mutane.
Hukumomi a matakin jiha da tarayya sun sha fadin cewa suna daukan matakan da suka dace wajen shawo kan matsalar tsaro a jihar Kaduna da wasu jihohi da ke arewa maso yammacin Najeriyar.