À Najeriya ‘yan fashin daji na ci gaba da fadada ayyukansu ta hanyar zafafa kai hare-hare suna kisa suna kama mutane don neman kudin fansa.
Wannan yana zuwa ne lokacin da ‘yan bindiga suka kona gari kacokam tare da mamaye wani gari a Sokoto dake arewa maso yammacin kasar.
Yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da aika-aikarsu a arewacin Najeriya abu ne mai daure kai, domin tamkar babu matakan da ake dauka na dakile ayukkan duk da ko mahukumta na cewa suna daukar matakan.
Bayan kona matafiya 23 da suka yi a Isa dake gabashin Sokoto dake arewa maso yammacin Najeriya, a ranar Asabar ta karshen makon da ya gabata sun kona wani gari kacokam dake yankin Kalmalo a Illela garin da ke makwabataka da Jamhuriyar Nijar.
Bello Isa Ambarura wakilin jama'ar yankin a majalisar dokokin jihar Sokoto ya ce aika-aikar yan bindiga tana wuce wuri.
“’Yan bindiga sun watse garin, dabbobinsu duk an kwashe kuma an kunnawa garin wuta. An kama wasu wasu kuma su rasu. Don Allah gwamnati ta tashi tsaye” In ji Ambarura.
Na tuntubi wani mazaunin Kalmalo, wanda ya ce jama'ar Illela suna cikin halin rashin tsaro.
Kokarin jin ta bakin jami’an tsaro ya ci tura.
A can ma yankin Isa duk da furucin da kwamishinan ‘yan sanda Kamaludden Kola Okunlola ya yi na cewa jami'an tsaro na sintirin hanyoyin yankin kusan safiya sai an tare hanya a kashe tare da sace mutane kamar yadda ya faru da maraicen ranar Lahadi inda ‘yan bindigar suka tare hanyar Isa zuwa Shinkafi suka kashe wani mutum.
Wadannan abubuwan da ke faruwa sun sa ‘yan Najeriya na ci gaba da mamakin ganin gwamnati na cewa tana kokarin kare rayukan jama'a kuma ga rayukan nata salwanta.
Farfesa Bello Badah mai sharhi ne akan lamurran yau da kullum.
“Shugabanci amana ne, wadannan mutane amana ne, har an sa sun fara fid da rai da cewa gwamnatin tarayya da ta jihohi da shugabannin suna iya masu wani abu.”
Wannan hari na yankin Illela na zuwa ne yayin da wata tawagar da shugaba Muhammadu Buhari ya tura jihar ta Sokoto ta kammala ziyarar jaje kan hare-haren da aka kai a ‘yan kwanakin nan.
Tawagar Shugaban kasar wadda ta kumshi manyan jami’an tsaron karkashin jagorancin Janar Mohammed Babagana Munguno ta kammala ziyarar da ta kai Kokoto da Katsina.
“Ba ma Sokoto kadai ba, dukkan inda aka samu irin wannan kazamin barna wanda wadannan ‘yan ta’adda suka yi wa ‘yan Najeriya, gwamnatin mai girma Muhammadu Buhari ta kan aika mutane a je a yi wa jama’a jaje a nuna rashin jin dadi kuma a yi musu tabbacin cewa an kawo karshen wannan al’amarin.” Ministan kula da ayyukan ‘yan sanda Mohammed Maigari Dingyadi ya fadawa Muryar Amurka bayan ziyarar.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5