Maharan dai sun auka gonar mai martaba Sarkin Sudan na Kontagoran ne Alh. Sa’idu Namaska da ke kauyen Udara da tsakiyar ranar alhamis din nan inda bayan sun kashe wadan nan mutane su kavyi awon gaba da shanu masu yawa mallakar sarkin.
Shugaban Karamar Hukumar Ta Kontagora Hon. Shehu S. Pawa yace a halin yanzu karamar hukumar na cikin tashin hankali.
Alh. Shehu Yusuf Galadima Galadiman Kontagoran ya ce masarautar na cikin kaduwa saboda akwai bukatar daukar matakin shawo kan wannan matsala ta rashin tsaron.
Karin bayani akan: jihar Neja, Kontagoran, Nigeria, da Najeriya.
Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai rundunar 'yan sandan jihar Nejan ba ta ce komai ba akan wannan sabon harin, to amma sakataren gwamnatin jihar Alh. Ahmed Ibrahim ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Wannan dai yana zuwa ne kwana daya bayan da 'yan bindigar suka kashe wasu sojojin Nigeria guda uku a kauyen Liballe dake kusa da Kontagora.
Saurari cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5