Bayanai daga ‘ya’yan kungiyar Boko Haram da suka tsere suka kuma mika kansu ga jami’an tsaro, sun yi nuni da cewa mutanen sun sulale ne daga sansanoninsu ba tare da sanin shugabanninsu ba, inda suka yi ta tafiya daga wani gari zuwa gari kafin har su kai Maiduguri.
"Sun yi tafiya ne daga wannan kauyen su je wannan kauyen." In ji wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda Biu wanda ya zanta da wasu daga cikin mutanen.
A lokacin ganawar da manema labarai, ‘yan kungiyar ta Boko Haram wadanda yawansu ya kai 70, sun ce sun tsaida shawarar ficewa daga kungiyar ne domin sun gane cewa, dabi’unsu ba kan hanya suke ba.
Wani abu da har yanzu ba a tantance ba shine ko mutanen da suka mika wuyan na wane bangaren kungiyar ta Boko Haram ne.
"Wannan shine har yanzu ba mu samu bayanai ba kuma bai fito fili ba ko na wane bangare ne, amma ko shakka babu sun tabbatar mana cewa su 'yan Boko Haram ne." Haruna ya bayyana.
A bara kungiyar ta dare zuwa gida biyu, da bangaren Abu Musab al Barnawi, mutumnin da kungiyar IS ta ayyana a matsayin sabon shugaban kungiyar da kuma bangaren Abubakar Shekau da ya jima yana jagorantar kungiyar.
A farkon makon nan ne rundunar tsaron Najeriya ta Operation Lafiya Dole a garin Maiduguri ta nunawa manema labarai wadansu mutane 57, wadanda ta ce ‘yan kungiyar Boko Haram ne da suka watsar da makamansu, suka kuma mika kansu da kansu ga jami’an tsaron.
Ta kuma ce mutanen su 70 ne amma ya zuwa lokacin hada wannan rahoto 57 aka kammala tantancewa.
Saurari hirar wakilinmu a Maiduguri Haruna Dauda Biu da Ibrahim Ka'almasi Garba domin jin cikakken bayanin yadda mutanen suka mika wuya:
Your browser doesn’t support HTML5