Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Banga Sun Shiga Hannun Jami'an Tsaro


‘Yan Sandan jihar Neja sunce sun kama ‘yan banga biyu da ake zargin suna da hannu a rikicin da yayi sanadiyyar mutuwar wasu mutane a Kontagora.

Rundunar ‘yan Sandan jihar Neja ta cafke wasu ‘yan banga biyu da ake zargin suna da hanu wajan hadasa rikicin da yayi sanadiyar hallaka mutane tare da hasarar dukiya a garin Kontagora.

Da Yammacin Alhamis din data gabata ne dai wasu matasa a Komtagora suka fusata suka kona ofishin ‘yan bangan saboda kisan gillar da suka ce ‘yan bangan sun yiwa wani matashi, alamarin da ya jawo zaman dar dar a garin na Kontagora.

Kakakin ‘yan Sandan jihar Neja, DSP Bala Elkana, y ace rundunar na ci gaba da bincike kuma zasu tabbatar an hukunta duk masu hannu a tashin hankalin da ya afku a garin Kontagora.

Da muryar Amurka ta tuntubi shugaban kungiyar ‘yan banga na jihar ta Neja, mataimakin Sufeto janar na ‘yan Sanda mai ritaya Ibrahim Machi, y ace bashi da cikakken bayani kawo yanzu.

A halin da ake ciki Gwamnatin jihar Neja, ta nuna rashin jindadinta akan wannan alamari a saboda haka ma take kiran jama’a da a kai zuciya nesa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG