A yayin da ake ta tattara sakamakon zaben gwamnoni a fadai Najeriya, haka yake a jahar Adamawa, Ibrahim Abdul’aziz ya aiko da rahoton cewar an sami sakamakon kananan hukumomi 8 cikin 21 a yayin da ya hada rahoton.
T a bangaren wakilan jam’iyu kuma, Barista AT Shehu kwamishinan shari’a na Jahar Adamawa kuma shi ya wakilci jam’iyar PDP yayi Karin bayani musamman irin yadda yakeji a yanayin fitowar sakamakon zaben sai y ace;
“Abin da yafi bani farin ciki shine yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana kuma babu inda ma’aikatan zaben suka ce ansami matsala. Kuma duk wanda ya lashe zabe a jahar Adamawa ko a jam’iyar PDP ko APC duk dai ‘yan Adamawa ne haka ma Nijereiya gabaki daya, bukatar mu wanda zaizo ya taimakawa talaka.”
A jahar Taraba kuma yayin da ake kokarin hada sakamakon zaben, takaddama ce ta kaure a yankunan Wukari, Ibbi da kuma Takum inda shaidu sukia bayyana cewar an hallaka mutum guda a yayin da aka budewa ma’aikatan zaben wuta.
Karamar hukumar Ibbi kuma an kada kuri’a amma maluman zaben sun nemi hana shiga da sakamakon.
Daga karshe Ibrahim Abdul’aziz ya ruwaito mana cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jahar SP Joseph Kuji yace anyi zabe cikin zaman lafiya. Bangaren jahar Adamawa kuma rundunar ‘yan sandar tayi amai ta lashe ne kamar yadda ta janye dokar tabacin da sanya tun daga ranar lahadin nan zuwa ranar talata.
Your browser doesn’t support HTML5