Wadansu mutane sun gamu da hadari a jihar Yobe a kan hanyarsu zuwa kada kuri’a , daga inda suke gudun hijira sakamakon matsalar tsaro da suke fuskanta.
Mutanen kimanin sittin da suka fito daga garin Gundu dake karamar hukumar BI;u ta jihar Borno, yanzu haka suna kwance a asibiti inda suke jinya.
A halin da ake ciki kuna, yau za a gudanar da zabukan gwamna da na ‘yan majalisa a kananan hukumomin Bama da Gala da Ganzai da kuma Goza. An soke zabe a wadannan kananan hukumomin ne jiya sakamakon kai kayan zaben cikin kurarren lokaci da aka dangantak da sake buga katunan zabe sakamakon rashin sa jam’iyar Labor a katunan da aka buga da farko.
An gudanar da zabuka a sauran kananan hukumomin cikin kwanciyar hankali. An gudanar da zaben a sansanin ‘yan gudun hijira a duk fadin jihar, inda ‘yan gudun hijiran suka bayyana gamsuwa da zaben suka kuma yi alkawarin amincewa da sakamakon zaben.
Da yake stokaci dangane da zaben jim kadan bayan kada kuri’arsa, gwamnan jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya bayyana gamsuwa da yadda aka sami ingancin na’urar tantance mai kada kuri’a da suka sami matsala a wadansu mazabu, makonni biyu da suka shige.
Ga ci gaban rahoton