Wani matashi ya rasa ranshi a wata mazaba dake yankin Ali Kazaure cikin garin Jos bayan kamala zaben da aka gudanar lafiya a kusan dukan mazabun jihar.
Kakakin rundunar tsaro ta musamman a jihar Plato Kaftin Ikedichi Iweha ya bayyana cewa, jami’an tsaro sun sami labarin cewa ana tashin hankalin a mazabar inda wani ya nemi yin arangizan kuri’u. Yace da jami’an tsaron suka tafi domin kwantar da hargitsin sai matasa suka shiga jefe jefe da yunkurin kwace makaman jami’an tsaro.
Wani wanda lamarin ya faru a ganin idonshi, yace matashin yana bin layi ne yana rabawa masu kada kuri’a kudi da madara da nufin sayen kuri’u lokacin da jami’an tsaro suka iso, ya zubawa wani daga cikinsu ruwan madara a ido ya gudu, su kuma suka harbe shi yam utu.
A jihar Plato ma kamar sauran jihohi, an fuskanci rashin fitowar jama’a a zaben gwamna da na ‘yan majalisa da aka gudanar a jihar Plateau. Binciken Muryar Amurka ya nuna cewa, ba a sami fitar jama’a sosai ba a zaben idan aka kwantata da na shugaban kasa da aka gudanar makonni biyu da suka shige.
Wadansu da Wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji tayi hira da su sun bayyana cewa sun gamsu da yadda aka gudanar da zaben duk da yake an fuskanci rashin fitar jama’a.
Ga cikakken rahoton