Auwal ya ce daga wancan lokacin da aka yi hira da shi, zuwa yanzu akwai karin ci gaba, yana mai cewa, babu abin da zai cewa masoyansa musammam ma 'yan Saudiya wadanda suke nuna masa kauna.
Ya ce tun da farko ya fara waka ta nanaye kafin ya lura da cewar wakar biki na daga cikin abubuwan da ke taimakawa rayuwarsa.
Lamari ya ce sanadiyar waka a yanzu har ta kai da wani gidan rediyo a jihar Kano ya dauke shi aiki a fannin Nishadi, kuma a halin da ake ciki ma a yanzu ya koma makaranta inda yake koyan aikin jarida sakamakon wannan aiki da ya samu.
Mawaka 'yan Makkah kamar yadda yake cewa sun tallafa masa matuka ta hanyar ba shi kyaututtuka, wanda hakan ya taimaka masa wajen inganta sana’arsa.
Ya kara da cewa, ya gwada wasu sana’o'in hannun amma a dukkanin sana’o'in babu wanda ya tsaya masa yake kuma jin dadinsa kamar waka.
Auwal Lamari kuma yi kira da kuma jan hankalin mawaka, da su kasance suna da aikin hannu a gefe baya ga sana'ar ta waka, su kuma rike sana’arsu tsakani da Allah.
A saurari cikakken rahoton wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.
Your browser doesn’t support HTML5