Yadda Rundunar Sojin Najeriya Ta Gudanar Da Ayyukan Raya Ilimi A Cross Rivers

Taron Bude Ayyukan Da Rundunar Sojin Najeriya Ta Yi A Jihar Cross Rivers.

Rundunar Sojin dai ta gudanar da ayyukan raya ilimin ne domin kara kulla alaka da fararen hula.

A wani mataki na kara yaukaka fahimtar juna tsakaninta da fararen hula, Rundunar Sojin Najeriya ta gudanar da wasu aikace aikace a wata makarantar Sakandare da ke Oban a karamar hukumar Akamkpa da ke jihar Cross Rivers.

Cikin aikace aikacen da Rundunar sojin ta gudanar a makarantar, ya kunshi sake fasalta dakunan gwaje-gwajen kimiyya uku da kuma gina jerin bayi don bai wa dalibai damar samun kyakkyawan yanayi koyo.

Taron Kaddamar Da Ayyuka A Makarantar Sakandaren Oban da ke Karamar Hukumar Akamkpa A Cross Rivers

Da yake jawabi yayin kaddamar da ayyukan, Babban hafsan hafsoshin mayakan Najeriya, Laftanar Janar Farouk Yahaya, wanda shugaban sashin inganta alaka da fararen hula na rundunar Manjo Janar MG Kangye ya wakilta ya bayyana cewa aikin wani bangare ne na irin gudunmuwar da rundunar ke bayarwa al'ummu daban-daban a kasarnan a matsayin tukwici na irin goyon baya da hadin kai da fararen hula ke basu.

Janar Farouk Yahaya ya kara da cewa akwai tsananin bukatar inganta alaka tsakanin sojoji da fararen hula musamman a wuraren da mayakan dake gudanar da aikace aikace, yana mai cewa kwadayin kara samun hadin kai da goyon bayan mutanen yankin nema ya sa aka gudanar da ayyukan.

Daliban Makarantar Sakandaren Oban da ke Karamar Hukumar Akamkpa A Cross Rivers 1

Wannan dai ya yi sanadiyyar kai aikin garin kuma dan asalin yankin, Manjo Janar VO Offiong ya bayyana cewa makarantar ta kasance cikin mummunan yanayi kafin babban hafsan ya kawo masu dauki, al'amarin da ya sanya matukar farin ciki da jin dadi ga zukatan mutan yankin.

Bisa al'ada dai dama rundunar sojojin Najeriya na gudanar da ayyukan jinkai da na raya kasa da ya shafi bangarorin hanya, ilmi, ruwan sha, lafiya, tallafin kayan masarufi ga al'ummun da suke gudanar da ayyuka a cikinsu musamman fafatawa don samun hadin kan fararen hula a yankunan.

Daliban Makarantar Oban da ke Karamar Hukumar Akamkpa A Cross Rivers

Alal misali a ‘yan kwanakin nan rundunar sojin ta gina hanya a wasu al'ummun Maraba da ke jihar Nasarawa, ta yi aikin samar da ruwa a Fika da ke jihar Yobe, aikin kula da lafiya ga wasu al'ummun jihar Ogun gabanin wannan gyaran makaranta a jihar Cross Rivers.