A lokacin da hadarin ya auku ma’aikatan ceto sun yi kokarin kubutar da wadanda suka tsira daga bala’in wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 30, a cewar rundunar 'yan sanda jihar.
Daruruwan masu ibada ne suka taru a cocin, mai suna Reigners Bible Church, wacce ba a kammala gininta ba, a lokacin da rufin mujami’ar ya rufta.
Ana shirin nada shugaban cocin ne a lokacin da lamarin ya auku.
Rahotanni dai sun ce akalla mutane 60 ne suka rasa rayukansu, amma jami’an tsaro sun ce sai an kammala aikin kwashe baragizan za a tabbatar da ainihin adadin.
Gwamnan ta jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel ya na cikin wadanda suka halarci taron cocin a lokacin da hadarin ya auku, amma dai ya fita babu ko kwarzane.
Wani kakakin gwamnan jihar ya ce an kaddamar da bincike na musamman kan wannan hadari.
domin jin cikakken bayani kan yadda hadarin ya auku, saurari rahoton wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Lamido Abubakar Sokoto:
Your browser doesn’t support HTML5