Shugaban Senegal Macky Sall shi ya kira shugabannin kasashen Afirka tare da shugabannin kungiyoyin duniya daban su halarci taron.
Kakakin fadar shugaban kasar Najeriya Malam Garba Shehu ya yi karin bayani akan taron. Yace batutuwan da suka shafi tsaro a Afirka da yaki da ta'adanci da sace sace da fashi da jiragen ruwa suna cikin abubuwan da taron zai tattauna a kai.
Ba shugabannin kasashe ba ne kawai zasu halarci taron ba. Akwai ministocin tsaro da ministocin da ayyukansu suka shafi zaman lafiya da makamantansu da zasu halarci taron. Haka ma hafsoshin dakarun kasashen zasu kasance a wurin taron. Kowannensu zai bada gudummawa akan irin yakin da za'a yi da ta'adanci da sauran matsalolin da suke kalubalantar nahiyar.
Hadin kai tsakanin kasashen zai taimaka wajen yaki da ta'adanci da sace sace da fashi akan teku da yanzu kasashe da dama a Afirka suna fama dasu..
Wani masanin tsaro Dr. Bawa Abdullahi Wase yace duniya ta soma dunkulewa wuri guda. Shugabannin Afirka sun soma gane makarkashiyar da ake yi masu da inda barna ke shigowa. Tarurukan su ne zasu taimaka a dinke barakar da ta barke a wurare daban daban.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.