Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kula da Lamuran Sufuri Zata Kawo Tsimin Kudi


Ginin majalisun tarayyar Najeriya
Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Kudurin da yanzu yake gaban majalisar dattawa idan ya zama doka za'a sami tsari mai kyau da hukumar da zata kula da lamuran sufuri a Najeriya hakan kuma zai kawo tsimin kudi.

Dan kwamitin sufuri na majalisar Dattawa Sanata Ali Ndume shi ya bayyana hakan yayinda yake magana a taron sauraren ra'ayin jama'a kan kudurin kafa hukumar kula da lamuran sufurin Najeriya.

Kudurin ya zo daidai da lokacin da gwamnatin tarayya ta hana shigo da motoci ta kan iyakokin kasa daga farkon badi.

Don nasarar kafa wannan hukumar a ra'ayin ministan sufuri Rotimi Amechi shi ne a mika aikin ga hukumar sufurin jiragen ruwa ta juye zuwa Hukumar Sufurin Najeriya domin kula da abubuwan da ake shigowa ko fita dasu ta hanyar teku.

Rotimi Amechi yace sun yi magana da majalisar wakilai wadda ta mikasu hannu kwararru domin sake duba kudurin wanda zai canza hukumar jiragen ruwa ta zama ita ce hukumar sufurin Najeriya.

Yayinda yake magana bayan taron, tsohon daraktan sayar da hannun jarin kamfunan gwamnatin Najeriya Ibrahim Muhammad Kashim yayi sharhi akan muradun gwamnatin Najeriya na son rage kashe kudi ta hanyar karawa hukumar hada hadar jiragen ruwa karfi ta zama mai kula da sufurin Najeriya maimakon kafa wata sabuwa. Yin hakan zai kara arzikin kasar fiye da abun da ake samu daga man fetur.

Ita hukumar hada hadar jiragen ruwa ta fadada ayyukanta da kafa tasoshin kan tudu don tallafawa wadanda ba sa gefen teku.

Ga rahoton Nasru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG