Yadda Rikicin Cikin Gida Ke Ci Gaba Da Dabaibaye Jam'iyyar APC

Buhari Ya Gana Da Shugabannin APC

Matsalolin cikin gida na kara ta'azzara a tsakanin jam'iyyar APC, du da cewa shugaban Najeriya ya kafa wani kwamiti karkashin tsohon gwamnan jihar Legas, Ahmed Bola Tinubu, domin sasanta 'ya'yan jam'iyyar.

Jam’iyyar APC a Najeriya na ci gaba da fuskantar babban kalubale, ganin yadda jam’iyyar ke kara fuskantar matsaloli tsakaninta da ‘ya ‘yanta.

A kwanakin baya shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nada Bola Ahmed Tinubu, jigo a jam’iyyar, da ya zagaya jihohin da ake da matsaloli tskanin ‘yan kungiyar, da zummar magance hakan.

Wani ma’abuci sauraren sashen Hausa na Muryar Amurka, Shehu Diye-diye, ya ce abubuwan da wasu ‘yan jam’iyyar ke yi na iya zama sanadiyar gurguncewar jam’iyyar.

Ya ba da misali da ire-iren abubuwan da ke faruwa a jihar Kaduna, inda ake zargin gwamnan da rusa wani gini da ke dauke da ofishin reshen 'yan adawan na ‘yan jam’iyyar.

Haka kuma hukumomi a jihar ta Kaduna, sun bukaci Sanata Sulaiman Hukunyi, da ya biya kudaden Haraji na daya daga cikin gidajen shi, da ke birnin Kaduna har na kudi sama da naira miliyyan 30.

Baya ga haka, tsige Sanata Abdullahi Adamu, da aka yi a matsayin shugaban kungiyar sanatocin Arewa, ya kara bayyanar da rashin jituwa a tsakanin ‘yan-jam’iyyar ta APC.

Sai kuma matsalar wanke shugaban majalisar dattawa Dr. Bukola Saraki, da aka yi na laifin kin bayyanar da kadarorin shi gabanin kama aiki.

Sai dai Mai Mala Boni, sakataren kungiyar ta APC, ya ce ai haka siyasa ta gada yana mai cewa dambarwar ta ciki gida, ba za ta saka jam’iyyar cikin matsala ba.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya domin jin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Rikicin Cikin Gida Ke Ci Gaba Da Dabaibaye Jam'iyyar APC - 3'00"