Masu garkuwa da mutane ne suka yi dirar mikiya a wani gari a cikin karamar hukumar Wurno da ke jihar Sokoto, kuma suka yi awon gaba da mutane.
Bayanan da Muryar Amurka ta samu sun nuna cewa da misali karfe 12 da mintuna ne na dare masu satar mutane suka afkawa garin Gidan Modi cikin karamar hukumar mulkin Wurno, inda suka nufi gidan wani Alhaji amma basu tarar da shi ba, sai suka yi awon gaba da matar sa da wasu mutane biyu da suka kama a garin.
Dan uwan wadanda aka yi garkuwa da su, Malam Haruna, ya ce anyi amfani da lambar wayar ‘yan uwansa aka kirawo shi aka ce su gaggauta su kawo kudin fansa, idan ba haka ba za su kashe su, kana su gaya musu wurin da za su je su dauki gawarwakin.
Ya kara da cewa sai da ya kai kudin fasa sannan masu garkuwa da ‘yan uwannasa suka bashi su.
Kantoman karamar hukumar Wurno, Ladan Muhammad Wurno, ya ce da samun rahoton zuwan ‘yan bindigar ya yi kokarin sanar da hukumomin tsaro, amma kafin jami’an tsaro su kai dauki har sun tafi.
Muhamad Wurno ya kara da cewa jama’a su kara saka ido kan baki da kuma mutanan da suke kashe kudade kuma basu da aiki domin kai wa jami’an tsaro.
Wannan satar mutanen na zuwa ne lokacin da babbar kotu mai daraja ta 3 a Sakkwato ta yanke hukumci ga masu satar mutane da aka gurfanar gaban ta su hudu inda ta baiwa kowane su shekaru 30 gidan kaso.
Masanin harkokin tsaro, Detective Auwal Bala Durimin Iya, ya ce yana da kyau a rika yayata hukumcin shari'ar da ake yiwa ‘yan ta'adda ko da zai zama darasi ga sauran su.
Amma ci gaba da tabarbarewar tsaro a arewacin Najeriya yasa malaman addinin musulunci sun soma haduwa kan yin addu'o'in neman samun sauki daga Allah.
Saurari cikakken rahoton Muhammadu Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: Arewacin Najeriya, da Sokoto.