Duba da kalubalen tsaro irin na satar mutane don neman kudin fansa ko fashi da makami ala tilas ya sanya yan Najeriya masu sukuni yin bulaguro ta jiragen sama don kaucewa irin abubuwan da kaje su komo.
Amma shima bulaguro ta hanyar jiragen saman na da nasa irin matsalolin musamman irin yawan jinkiri da ake samu kafin tashin jiragen a daidai lokacin da aka tsara tashin.
Sau tari matafiya na shafe sa'o'i' da dama suna jiran tsammanin warabbuka a filin jirgi don tashi zuwa wurare daban daban a cikin kasar, al'amarin da jami'an kamfanonin jiragen kan baiwa matafiyan hakurin jinkirin da ake samu duk da yake lamarin ke ci gaba da ta'azzara.
To sai dai kuma bisa ga dukkan alamu ba wani mataki da kamfanonin ke dauka don kawo karshen wannan matsala da a baya bayannan ke neman samun gindin zama a tsakanin kamfanonin jiragen saman kasar.
Matafiya da dama da Muryar Amurka ta zanta da su a filin jirgin saman sun nuna damuwarsu bisa yadda ake samun wannan jirgin abin da suka ce na shafar uzururrukansu.
A bayanin sa, daya daga cikin jami'an kamfanonin jiragen ya ce irin wannan matsala na faruwa ne saboda dalilai daban daban, alal misali yace idan jirgi daya ya sami matsala cikin jerin jiragen kamfani guda, to baki dayan tsarin sufurin wannan rana zai sami matsala.
Duk kokarin jin ta bakin hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama ta Najeriya a lokacin hada wannan rahoton bai yi nasara ba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5