Yadda Mata Ke Gyara Ragowar Abinci Domin Tallafawa Mabukata

A yau dandalinVOA ya samu bakuncin wasu mata dangane da yadda suke sarrafa ragowar abincin da aka yi buda baki da shi duba da yadda aka fara rage cin abinci da zarar an yi buda baki.

Malama Maryam Tijjani, daya daga cikin matan da suka bakunci dandalin namu cewa ta yi da zarar abinci ya ragu a mafi akasari zubarwa ake yi sakamakon rashin almajirai da basa samu a yankinsu, sannan mafi yawan makwabtanta masu hannu da shuni basa bukatar ragowar abinci.

Ta ce duk da halin matsin da ake fuskanta almajirai basa shiga sashin su, ita kuwa malama Aisha Mohammad cewa ta yi sabanin malama Maryam, ita a yankinsu suna samun almajirai da suke baiwa ragowar abinci ba tare da sun takura kansu wajen kaiwa makwabtansu ba.

Sannan ta ce sukan dumama abinci su kai wa ‘ya’yan makwabta sannan tana baiwa almajirai bayan shan ruwa da kuma asuba domin yin sahur, dalilin haka basa barnar abinci domin akwai mabukata da dama.

Ita kuwa Maryam, cewa ta yi, baya ga ragowar abinci a halin yanzu ta rage hannun abinci sannan ta canza nau’ikan abincin da ta ke yi inda a yanzu ta fi maida hankali wajen sarrafa abinci mara nauyi wanda zai yi saurin narkewa kuma ba zai takurawa mutum ba kuma wanda za’a iya cinyewa a lokaci guda.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Mata Ke Gyara Ragowar Abinci Domin Tallafawa Mabukata