Yadda Masu Zanga Zangar Nuna Goyon Baya Ga Trump Suka Abka Cikin Ginin Majalisar Kasa.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda aka fidda 'yan Majalisar Dokokin Amurka daga ginin Majalisa, Capitol Hill, bayan da magoya bayan Shugaba Donald Trump masu zanga-zanga suka danna ciki.

Mafusatan magoya bayan Shugaba Donald Trump sun fantsama cikin ginin Majalisar Dokokin Amurka a ranar Laraba a lokacin wata zanga-zanga. Turump ya yi kira ga zaman lafiya bayan an kammala rikicin amma bai bukaci magoya bayansa su watse ba. Tun daga farko ya ba su izinin zuwa titin Capitol Hill.

Magoya bayan Shugaban sun yi zanga-zangar ne da nufin dakile shirin mika mulki cikin lumana, sai da aka yi hanzarin fitar da ‘yan majalisar daga ginin.

Trump ya yi kiran da a kai zuciya nesa, a yi zaman lafiya bayan an kammala rikicin. Amma bai bukaci magoya bayansa su watse ba. Tun daga farko ya ba su izinin zuwa titin ginin Majalisar, wato Capitol Hill.

Haka zalika, magoya bayan Shugaba Donald Trump kimanin 300 ne suka hallara a harabar ginin Majalisar Dokokin jahar Michigan a ranar Laraba, yayin taron hadin gwiwar Majalisar da aka kira a Washington, D.C, don tabbatar da kuri’ar Kwalejin Zabe da Joe Biden ya lashe.

A halin da ake ciki kuma an kafa dokar ta baci a fadin Birnin Washington D.C. inda har yanzu magoya bayan Trump din ke kara kaina.