Wannan mataki da Gwamnatin Ahmed Bola Tinubu ta dauka na cire tallafin man fetur abu ne da ya janyo cece kuce a shiyyoyi daban daban na Kasar musamman ma a tsakanin manoma da a yanzu haka suke samun turjiya wajen kai kayan amfanin gona garuruwa daban daban saboda karin kudin man fetur.
A shiyyar Arewa kungiyoyin manoma da dama sun hada kansu wuri guda a karkashin wata hamshakiyar manomiya wacce ta ke zaune a Jihar Kalifoniya ta Kasar Amurka, Amina Temitope Ajayi, domin su kai kukan su ga Gwamnatin tarraiyya saboda a kawo sabbin dabarun noma a Kasar.
Temitope ta ce Najeriya kasa ce da Allah yayi wa albarka, saboda tana da kasa mai kyau da za a nome komi kuma yayi kyau sosai, ga kuma mutane masu hazaka. Temitope ta ce ta zo ne domin ta taimaka wajen kafa wata cibiya da za ta koya wa mata da matasa dabarun noma na zamani, kuma tuni ta samu manyan manoma na kasar Amurka da suka nuna sha'awar su wajen sayan kayan amfanin gona da ake nomewa a Najeriya, irinsu dawa,waken soya da sauran su, saboda haka an riga an samar wa kayan amfani gonan kasuwa.
Shugaban Manoman Dawa Mohammed Babayo Maina ya ce sun ji dadi da aka cire tallafin man fetur tunda Gwamnati ta riga ta yi alkawali cewa za ta zuba kudin a bangaren noma domin kasa ta wadatu da abinci.
Shi ma Hassan Abubakar ya ce akwai abin dubawa a harkar noma idan babu mai. Hassan ya ce dama noma ba zai yiwu ba sai da mai, kuma idan an ce mai ba zai samu ba, to dole sai ya tabi amfanin gona, amma idan Gwamnati ta dauki kwararan matakai kan bunkasa noma, to lallai manoma za su ji dadi.
Shi kuwa Alhaji Abubakar Danmalikin Kebbi, ya yaba ne da matakin kafa cibiyar horar da dabarun noma inda ya ke cewa dama babu noman zamani a Najeriya har yanzu, tunda manomi sai ya dauki injin da hawiya a hannunsa kafin ya je yayi noma, kuma ga matsalar taki ga kuma matsalar man fetur a yanzu. Dan maliki ya ce ko a lokacin da ake sayar da mai akan Naira 200, talaka bai yi noma cikin dadi ba. Saboda haka yayi kira ga Gwamnati da ta kawo tallafi da wuri, saboda manoma su hada koyon noman zamanin da yin na gargajiya a lokaci daya, saboda a samu amfaninsa.
Manoman da ma masharhanta sun yi ittifaki cewa, idan an aiwatar da cire tallafin mai yadda ya kamata, yana iya zama muhimmin abin gado na Gwamnatin Tinubu, wanda zai bambanta shi da Gwamnatocin baya.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5