Sanatoci 57 ne suka amince a dora laifin akan Trump, yayin da 43 suka nuna akasin hakan, yunkurin da ya gaza samar da biyu cikin kashi uku na rinjayen da ake bukata kafin a tsige shugaban kasa.
An tuhumi Trump ne da laifin cewa shi ya tunzura magoya bayansa suka mamaye ginin majalisar a ranar 6 ga watan Janairu, jim kadan bayan wani jawabi da ya gabatar.
An dai kwashe kwana biyar ne ana zaman sauraren muhawarar a zauren majalisar.
A Wannan kada kuri’a da majalisar ta yi a ranar Asabar, bakwai daga cikin ‘yan Republican 50 ne suka marawa ‘yan Democrat baya domin ganin an tsige Trump.
Bayan da aka wanke shi, Trump ya fada cikin wata sanarwa cewa, “wannan wani babi ne bi-ta-da-kullin siyasa mafi girma a tarihin kasarmu. Babu wani shugaban kasa da ya taba fuskantar wani abu makamancin wannan.”
A nashi bangaren, shugaba Joe Biden cikin wata sanarwa ya ce, “duk da cewa kada kuri’ar da aka yi a karshe bai kai ga an same shi da laifi ba, dalilin da ya sa aka tuhume shi bai sauya ba.”