Wani bam da ya tashi a wani wajen sayar da shayi a wani kauye a arewa maso gabashin Najeriya ya halaka mutum 19 tare da raunata wasu dozin biyu a wani babban hari na biyu cikin ‘yan makonni, kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana a ranar Alhamis.
Fashewar da aka yi a kauyen Kawuri da ke jihar Borno a yammacin ranar Laraba na daya daga cikin mafi muni a 'yan shekarun nan a yankin na arewa maso gabashin Najeriya, inda tashe-tashen hankulan da ake fama da su na masu ikirarin jihadi.
“An samu fashewar wani abu ne a wani rukunin sayar da shayi a Kawuri da misalin karfe 8:00 na daren jiya. Mun kwaso gawarwakin mutum 19 da kuma wasu 27 da suka jikkata.” Inji Ibrahim Liman, wani ‘dan kungiyar masu fafutukar yaki da Jihadi da ke aiki da sojoji, ya shaida wa AFP.
Babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin na ranar Laraba, amma kungiyar masu ikirarin jihadi ta Boko Haram kan kai ire-iren wadannan hare-hare.
Har yanzu ‘yan bindiga na kai harin kwantan bauna, da tayar da bama-bamai a gefen hanya da kuma yin garkuwa da su daga maboyar kauyuka, amma hare-haren bama-bamai a garuruwa da kauyuka a yanzu ba su cika faruwa ba a yankin na arewa maso gabas.