A jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin kasar, gwamnatin jihar ta hada hannu da wani shiri na L-PRES mai samun tallafi daga bankin duniya domin daukar matakan rage samun irin wannan matsalar.
Sau da yawa ake samun tashe-tashen hankula sanadiyar fadan manoma da makiyaya wanda wasu lokuta yakan kai ga asarar rayuka da dukiyoyi, duk da matakan da hukumomi ke dauka na magance aukuwar hakan.
Jami'in da ke kula da shirin L-PRES, Sirajo Abubakar yace shirin na da zummar fitar da wasu hanyoyi na zamani wadanda zasu taimaka wajen rage samun wadannan matsalolin.
An samar da wani kwamiti wanda zai yi aiki na sasanta manoma da makiyaya tun shekarar 1969 sai dai kwamitin ya zamo tamkar akwai-wa-babu, to sai dai shugaban kwamitin gudanar da wannan aikin a Sakkwato kuma kwamishinan kula da lafiyar dabbobi Aliyu Abubakar Tureta yace zasu baiwa marada kunya.
Wadanda matsalar ta fi shafuwa kai tsaye wato manoma da makiyaya sun ce sun shirya domin bayar da hadin kai ga kwamitin domin kwalliya ta biya kudin sabulu, domin sun gaji da rigima da juna.
To amma masu sharhi akan lamurran yau da kullum, kamar Farfesa Bello Bada na Jami'ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato yace muddin mahukunta ba su sanya gaskiya ga aikin wannan kwamitin ba, tare hukunta duk mai laifi, to ba za'a rabu da matsalolin ba.
Jihohi da dama a Najeriya har ma da wasu kasashe na samun irin wadannan tashe-tashen hankula tsakanin manoma da makiyaya, abinda kan kazamce wasu lokuta har ya dauki wata sigar tashin hankali mummana.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5