Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Fulani Sun Yi Taron Dawo Da Darajasu


Dr. Abubakar Umar Girei
Dr. Abubakar Umar Girei

Kungiyoyinn Fulani makiyaya sun yi gagarumin taron neman bakin zaren dawo da martabar su a idon duniya daga kashin kajin da wasu ke shafawa mu su.

ABUJA, NIGERIA - Kungiyoyin sun gudanar da taron karkashin kungiyar MIYETTI ALLAH a Abuja inda dukkan masu ruwa da tsaki su ka halarta. Taron ya nesanta dukkan Fulani daga ayyukan ta'addanci da nuna za a iya samun miyagu a kowace kabila.

Fulanin sun yi kira ga gwamnati ta rika hada kai da kungiyoyin Fulani wajen samar da maslaha.

Wakilin Lamidon Adamawa Dr.Abubakar Umar Girei ya ce in an ba su dama za a iya kawo karshen fitinar barayin daji a arewa "A gwada mu ko na mako daya ne a wata karamar hukuma za a ga sauyi"

Shi ma Shugaban kungiyar matasa makiyaya "JAM NDER FULBE" Kwamred Ahmad Muhammad Lamido ya ce su na daukar dukkan matakan raba baragurbi a matasan daga miyagun kwayoyi.

Gamayar kungiyoyin makiyayan karkashin jagorancin, Baba Usman Ngelzarma, da tsohon gwamnan Bauchi, Isa Yuguda, ta karrama shaharerren malamin Islama, Musa Yusuf Asadussunnah da sarautar Ardon Adalci don yanda ya ke wayar da kai ga fahimtar da al'umma halin da makiyayan ke ciki.

Asadusunnah ya nanata kiran hada kai a arewa don salama mai dorewa.

A nan Fulanin sun bukaci rushe dukkan kungiyoyin sa-kai da kan dau mataki ba tare da dogon bincike ba.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Kungiyar Fulani Sun Yi Taron Dawo Da Darajasu.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG