AGADEZ, NIGER - Taron da aka shafe kwanaki uku ana gudanar da shi ya samu halartar kungiyoyin makiyaya daga kasashe na yankin Sahel irinsu Chadi, Mali da kuma Burkina Faso.
Makasudin taron shine bitar halin da matsalolin tsaro suka jefa rayuwar makiyaya da yin barazana ga makomar sana’ar kiwo a wadannan kasashe na sahel.
Hamidou Sawadogo, daya daga cikin shugabannin makiyaya na Burkina Faso ya bukaci taimakon gwamnatocin kasashen yankin wajen shawo kan matsalolin tsaron dake rutsawa da su wajen gudanar da harakokinsu
Ra’ayi dai yana zuwa guda tsakanin shugabannin makiyayan game da kare batun kiwo a wadannan kasashen a cewar Malan Balma, wani makiyayi daga kasar Mali, ya ce akwai bukatar makiyaya su fahimta tare da kiyaye dokokin kasashen yankin wanda hakan zai basu damar gudanar da kiwon nasu ba tare da wata matsala ba saboda wadannan matsalolin na barazana ga makomar kiwo a kasashen.
Mahalarta taron dai sun fito da shawarwari na hanyoyin samar da mafita domin shawo kan wannan matsalar da ta taso ga sanar’ar kiwo.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna