A yau Talata 10 ga watan Disamba ake bikin tunawa da ranar ‘yancin dan adam a ko'ina a duniya, dalilin da ya sa masu rajin kare hakkin dan adam a Jamhuriyar Nijar suka shirya wata muhawara.
Muhawarar ta mayar da hankali ne kan kira ga hukumomi da jama’a da su yi nazarin hanyoyin samar da kariya ga jami’an fafutuka, sakamakon lura da hadarin da ke tattare da gwagwarmayar kare hakkin bil adama a yau a kasashe da dama.
Kare hakkin dan adam na daga cikin ayyuka mafi hadari a yau a duniya saboda yadda wasu ke farautar irin wadannan jami’ai da nufin kawo masu jinkiri a aikinsu.
Hakan ya sa hukumar kare hakkin dan adam ta CNDH ta shirya taron muhawara domin tattaunawa kan wannan batu.
Domin magance irin wadanan matsaloli, gwamnatin Nijar ta aika wa Majalisar Dokokin kasar wani kudurin dokar da ke hangen samar da kariya ga jami’an kare hakkin dan adam a wannan kasa, matakin da Mahaman Bachar na gamayyar kungiyoyin Reseau Esperence ke ganin ya yi daidai.
Kare hakkin dan adam, aikin sa-kai ne da ke daya daga cikin ginshikan dimokaradiyya, saboda haka mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Massaoudou Ibrahim ke jaddada muhimmancin jan hankulan jama'a game da nazari kan wannan rana.
Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana cewa jami’an fafutuka sama da 20 ne suka hallara a shekarar 2016 a dalilin aikin kare hakkin dan adam.
Dalilin kenan da hukumar kare hakkin dan adam ta kasa CNDH, tare da hadin gwiwar kungiyar Tarayyar Turai, da gamayyar REPPAD Nijar suka fara yunkurin nuna goyon baya ga Majalisar Dokokin kasar ta Nijar.
Saurari rahoto a sauti.
Your browser doesn’t support HTML5