Yadda Aka Yi Shagulgulan Bikin Cikar Sarkin Zazzau Shekara Daya Akan Karagar Mulki

Your browser doesn’t support HTML5

Masarautar ta Zazzau da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya, ta yi fama da matsalar hare-haren 'yan bindiga da ke garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
Sarkin Zazzau Mai Martaba Ahmad Nuhu Bamalli ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da taimakawa hukuma wajen yaki da matsalar tsaro. Mai Martaba Ahmad Nuhu Bamalli, ya yi kiran ne a wajen bikin cikar shi shekara guda akan karagar mulkin masarautar Zazzau. Wakilinmu Sani Shuaibu Malumfashi ya halarci bikin ga kuma rahoton sa.