Yadda Aka Rabawa Marayu Tallafin Kayan Sallah A Nijar

Taron Bada Tallafin Kayan Sallah Ga Marayu A Nijar 2

Kungiyar hadin kan kabilun Nijar wato NSC a takaice ta shirya bikin rarraba tufafin sallah da kayan abinci domin yara marayu da nufin ba su damar samun walwala kamar sauran yaran da iyayensu ke raye.

Wannan na zuwa a yayin da al’ummar Musulmin kasashen duniya ke shirye-shiryen bukin karamar sallah a wannan mako.

Yanayin tsaro a yankin Sahel wata matsala ce da ke bukatar gudunmowar kowane dan kasa dalili ke nan kungiyar ta shirya addu’oin zaman lafiya dabra da wannan buki.

Lura da yanayin damuwar da yara marayu ke tsintar kansu ciki a irin wannan lokaci na shirye shiryen sallah ya sa kungiyar hadin kan kabilun Nijar wato les Nigeriens Sont des Cousins ta shirya buki don rarraba wa irin wadannan yara tallafin tufafi da abincin sallah ta yadda za su samu damar yin shagulgulan karamar sallah cikin murna da annashuwa kamar yadda abin yake a wajen sauran takwarorinsu yara.

Taron Bada Tallafin Kayan Sallah Ga Marayu A Nijar 3

A hirar shi da Muryar Amurka, shugaban kungiyar NSC mai yaki da bambancin kabila a Nijar, Mahaman Lawali Ali Djibo, ya ce wannan koyarwa ce ta Annabi Muhammadu (S.A.W) da ya ce da wani da wanda yake taimaka marayu muna tare. Hakan yake nuna cewa muhimmanci maraya a cikin al’umma, to shi ne a kowace shekara su ke taimaka musu da abun da za su yi kayan sallah.

Ya ce wannan misali ne suke bayarwa kuma bai isa ba, ya kamata kowa ya sa hannunsa a taimaka wadannan marayun saboda wanda yake doran kasa gobe mutuwa zai yi ya bar nasa dan maraya.

Taron Bada Tallafin Kayan Sallah Ga Marayu A Nijar 5

Daya daga cikin iyayen marayun da yaronta ya samu tufafi, Malama Ramatou Abdou, ta ce wannan taimako ya yi kyau saboda abu ne da aka yi domin yaran da mahaifansu suka rasu.

Ta ce muna yi wa Allah godiya su ma muna gode masu saboda kokarin da suke yi. Yarona ya rasa mahaifinsa tun ya na da shekaru 4 a duniya kuma mahaifiyarsa ta rasu yau shekaru 12 da suka gabata, ban taba samun tallafin sallah ba sai a wannan karon, an ba mu shinkafa muna godiya.

Kamar yadda aka saba a irin wannan lokaci na gab da kulle goma ta 3 ta karshen watan azumin Ramadan kungiyar ta NSC ta tattara Malamai don sauke alkur’ani mai tsarki a matsayin wata gudunmowar neman mafitar matsalolin tsaron da ake fuskanata a yau.

Taron Bada Tallafin Kayan Sallah Ga Marayu A Nijar 1

A cewar Mahaman lawali Ali Djibo wajibi ne jama’a su rinka tuna wa da dakarun tsaro.

Wannan shine karo na 4 da kungiyar hadin kan kabilun Nijar NSC ke shirya irin wannan taro na aiyukan jin kai da nuna kishin kasa a albarkacin watan Ramadan ta hanyar tarbacen da ta ke samarwa daga wasu daidaikun mutane.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma :

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Aka Rabawa Marayu Tallafin Kayayyakin Sallah A Nijar.MP3