Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya umurci jami’an tsaro da su zakulo ‘yan bindigar da suka kashe mutum takwas, da raunata wasu da ke aikin hakar ma’adinin Kuza a yankin Kuru, da ke karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar.
A wata sanarwa da gwamnan ya fitar, ya nuna fushinsa kan yadda bata-gari ke neman hargitsa zaman lafiya a jihar da kuma sanya fargaba a zukatan al’ummarta
Kwamishinan yada labarai da sadarwa a jihar Filato, Mr. Dan Manjang ya ce wadanda aka kashen sun fito nemarwa iyalansu abinci ne yayin da ‘yan bindigar suka hallaka su.
Barrista Solomon Dalyop ya ce lamarin ya auku ne da misalin karfe bakwai na yammacin ranar Jumma’a.
Duk kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jahar Filato ya citura, duk da sako da Muryar Amurka ta aike wa kakakin rundunar, ASP Ubah Gabriel.
Karin bayani akan: ‘yan bindiga, Jihar Filato, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Jihar Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriya, ta sha fama da rigingimu masu nasaba da addini da kabilanci.
Har ila jihar ta yi fice da wuraren hakar ma’adinai da suka da kuza da sauran albarkatun kasa.
Saurare cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5