Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Makamai A Hannun Mutane Barazana Ne Ga Tsaron Kasa - Abdulsalami


Tsohon shugaban mulkin soji Abdulsalami Abubakar
Tsohon shugaban mulkin soji Abdulsalami Abubakar

Akwai bukatar samarwar jami'an tsaro kayan yaki na zamani.

Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar ya ce akwai damuwa matuka game da yaduwar makamai a sassan kasar, wanda aka kiyasta adadin kudinsu zai kai miliyoyin nairori.

Hakan a cewar Abdulsalam, wanda shi ne shugaban kwamitin wanzar da zaman lafiya na kasa, na kara haifar da tabarbarewar tsaro a kasar, abin da ya kai ga rasa rayukan mutum sama da 80,000 ya kuma sa mutum sama da miliyan uku suka tsere daga muhallansu.

Tsohon shugaban mulkin sojin ya bayyana hakan ne, a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Muryar Amurka.

A cewar Abdulsalam, kalubalen Najeriya na da fuskoki da dama, wadanda suka hada da rikicin Boko Haram, satar mutane, karuwar talauci, da kiraye-kirayen da ake yi na ganin an daidaita kasar daga bangarori daban-daban.

Ya kara da cewa akwai kuma batun barazanar yunwa da ke tasowa daga matsalar rashin tsaro, da manoma suke fuskanta, da dai makamantansu.

"Yawaitar dukkan nau'ukan makamai ba wai kawai a yankinmu gaba daya ba ne, musamman ma a Najeriya, yana da matukar damuwa. An kiyasta cewa akwai sama da irin wadannan makamai miliyan shida da ke yaduwa a kasar.

Wannan hakika ya ta'azzara rashin tsaro wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama" in ji shi.

Tsohon shugaban ya kara da cewa hukumomin tsaro za su iya yin aiki mafi kyau idan aka samar musu da manyan makamai, kayan aiki da kuma karin kudade.

"Mun yi imanin cewa dole ne Najeriya ta nemi mafita daga waɗannan matsalolin. Fatanmu a nan shi ne, ta hanyar ba da shawarwari ga gwamnati, za mu iya fara samun ƙwarin gwiwa tsakanin mutanenmu, don mu kasance tare."

Ya kara da cewa, suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun baiwa gwamnati shawara, yana mai cewa, gwamnati "ita ta san yadda take aikinta, kana ayyukan gwamnati suna da yawa ba wai kawai samar da tsaro ne aikinta ba akwai matsalolin ilimi, lafiya, hanyoyi da dai makamantansu."

"Saboda haka fatan shi ne, ba wai kawai mu yi ta kuka da jimami game da halin da muke ciki ba ne, amma za mu gabatar da wasu shawarwari na zahiri wadanda za su iya nuna hanyar ci gaba, shawarwarin da za su iya kara karfafa gwiwa a tsakanin mutanenmu da kuma tabbatar da cewa kasarmu ta ci gaba da zama daya."

Ana iya sauraron tattaunawar cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG