Yadda Aka Kama Jabun Magunguna A Jihar Kano Na Sama Da N150M

Hoton Jabun Magunguna Da Aka Kama a Kano

Hukumar Kula da Hakkin mai saye da sayarwa ta jihar Kano wato Consumer Protection Council ta kama wasu jabun magunguna na sama da Naira miliyan dari da hamsin.

Mukaddashin Shugaban Hukumar Kula da Hakkin mai saye da sayarwa ta jihar Kano Baffa Babba Dan'agundi ne ya bayyana haka, jim kadan bayan kama jabun magunguna a wani gurin ajiyar kaya da ke Karamar Hukumar Ungogo.

Baffa Dan-Agundi ya ce sun sami rahoton sirri daga wajen wani mazaunin yankin, wanda ya sanar da Hukumar irin hada-hadar jabun magungunan da ake aikatawa.

Shugaban hukumar mai rikon kwarya ya ce sun kai samamen ne da misalin karfe biyu na daren ranar Laraba bisa jagorancin sa.

Hoton Jabun Magunguna Da Aka Kama a Kano 2

Sannan ya yi kira ga al'umma da su ci gaba da taimakawa hukumar wajen sanar da ita bayanan sirri domin a kare lafiyar al'ummar jihar Kano.

Shugaban ya kara da cewa akwai tukwici na Naira dubu dari da hamsin ga duk wanda ya kawo rahoton bayanin wurin da ake hada-hadar jabun magungunan da jabun kayayyakin amfani na yau da kullum.