An kai su makawancinsu ne da ke makabatar sojoji ta unguwar Lugbe da ke Abuja babban birnin tarayya da safiyar ranar Alhamis.
Jirgin nasu mai suna Beechcraft King Air B350 ya fadi ne a ranar Lahadi a Abujar, a lokacin yana shirin zuwa gudanar da aikin tattara bayanan sirri domin kubutar da daliban makarantar Kagara da 'yan bindiga suka sace sama da mako guda.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa iyalan mamatan, abokan arziki da sauran wadanda suka halarci wannan jana’iza sun yi ta zub da hawaye a wani yanayi na ban tausayi.
Sojojin sun hada da Flight Lieutnant Haruna Gadzama, Flight Lieutenant Henry Piyo, Flying Officer Michael Okpara, Warrant Officer Bassey Etim, Flight Sergeant Olasunkanmi Oluwunmi, Aircraft Adewale Johnson.
Jana’izar har ila yau ta samu halartar manyan sojojin saman Najeriya da wasu manyan jami’an gwamnati.