Yadda Zabe Ya Wakana a Jihohin Sokoto Da Zamfara Da Kuma Kebbi

A jihar Sakkwato an sami fitowar jama'a sosai a runfunan zabe, sabanin jahohin Zamfara da Kebbi.

Sabanin mafiya akasarin johohin arewacin Najeriya, a jihar Sakkwato an sami fitowar jama’a sosai a runfunan zabe. Inda a wasu wuraren ma adadin masu zaben na kokarin zarta na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da aka gudanar makonni biyu da suka gabata.

wannan yasa duk da yake an soma zaben cikin lokaci, amma wasu runfunan zaben basu rufe ba har ya zuwa karfe biyar na yamma.

A iya cewar dai zaben ya gudana salun alun a mafi yawan runfuna, to amma kuma an sami hatsaniya da rigingimu a wasu wuraren sakamakon zafafar fafatawa tsakanin manyan ‘yan takara biyu na jam’iyyun APC Da PDP.

A jihar Zamfara dai zaben ya gudana tare da karancin fitowar jama’a, lamarin da yasa akasarin runfunan zabe suka rufe tun misalin karfe biyu na rana, to sai dai rohotanni sun nuna cewar ba’a sami gudanar da zaben ba a wasu yankunan dake fama da kalubalen tsaro musamman wuraren da al’ummar su suka tarwatse.

A jihar Kebbi ma an soma zaben cikin lokaci aka kuma kamala jefa kuri’a cikin lokaci, sakamakon karancin fitowar jama’a a zaben.

Saurari cikakken rohoton Murtala Faruk Sanyinna ya aiko daga Sakkwato.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Aka Gudanar Da Zabuka A Jihohin Sakkwato, Zamfara Da Kebbi 02'52"