Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Da Nakasassu Sun Fito Zabe A Jihar Niger


Mata da masu fama da lalurar nakasa na daga cikin dubban mutanen da sukayi tururuwa zuwa rumfunan zabe domin kada kuri'ar su a zaben Gwamna da 'yan Majalisar Dokokin Jihar Neja a Najeriya.

Masu fama da Nakasar da matan sunyi fatan wadanda Allah yaba cin zabe su maida hankali wajan kula da su.

Ana shi gefen dan takarar kujerar gwamna na jam'iyyar adawa ta PDP Alhaji Umar Nasko, ya ce zai rungumi kaddara a duk yadda sakamakon ya kasance, shima Gwamnan jihar Nejan Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce yana fatan za a kammala zaben lafiya kuma yayi kira da akwantar da hankali ga duk yadda sakamakon zaben yazo.

Amma ga jam'iyyar adawa ta ACD zaben yazo mata ne cikin yanayi na zaman makoki, a sakamakon rasa daya daga cikin 'yan takararta na Majalisar jiha daga yankin karamar hukumar Kontagora Adamu Musa wanda ya rasa ransa da yammacin Juma'ar nan a sakamakon hadarin mota.

Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Mustapha Nasiru Batsari daga Minna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG