Yadda Aka Gudanar Da Zabe a Jihar Filato

Kammala zaben gwamna da ake yi a jahar Filato na gudana cikin tsauraran matakan tsaro.

Tun da misalign karfe bakwai na safe ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta kai kayayyakin aiki a rumfunan zaben.

A rumfar zaben Jenta Mangoro, a karamar hukumar Jos ta Arewa, zaben ya gudana ne cikinkwanciyar hankali.

A rumfar zabe na Plateau Hotel Junction kuwa kalilan jama’a ne suka fito, saboda a cewarsu, yawancin mutanen dake rumfar basu ma san za a gudanar da zabe a rumfar ba.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Aka Gudanar Da Zabe a Jihar Filato - 3'45"