Alkalin babbar kotun jihar Adamawa, Justice Abdul'Aziz Waziri, ya dage karar da jam'iyyar MRDD da kuma dan takararta Eric Theman suka shigar na neman a soke zaben jihar bisa zargin ba'a saka hoton jam'iyyar ba akan kuri'ar da aka kada.
Bayan doguwar muhawara a tsakanin lauyan jam'iyyar ta MRDD, da kuma na bangaren hukumar zabe INEC,Justice Abdul'Aziz Waziri ya dage shari'ar har zuwa ranar Talata mai zuwa domin yanke hukunci kan ko kotun na da hurumin sauraron karar ko kuma a'a .
Haka nan alkalin ya umarci hukumar zaben da kada ta aiwatar da komi sai bayan yanke hukunci.
"Kasan mu a shirye muke mu kare abin da muka shigar gaban kotu don muna da shaidu da hujjoji, da wasu tabbatar da ikirarinmu don haka ba ma tsoro," a cewar Barista Adeyemi Pitan, lauyan MRDD da Eric Theman.
Shi ma dai wanda ya jagoranci lauyoyin hukumar zabe INEC, babban lauyan Najeriya Tanimu Muhammad Inuwa (SAN),ya nemi kotun ne ta yi fatali da karar tun da hukumar ba ta san da mai karar a matsayin wadanda suka shiga takarar gwamna ba, kuma ya ce kotun ba ta da hurumin sauraran wannan kara.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz: