Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Zargin Da Ake Yi Wa Sojojin Najeriya Lokacin Zabe


Janar Tukur Buratai
Janar Tukur Buratai

Hedkwatar sojojin Najeriya ta kafa wani kwamitin bincike karkashin jagorancin wani babban Hafsa Manjo Janar T.A. Gagariga, don binciko zarge zargen da ake yi wa sojin lokacin zaben 2019.

Kwamitin Wanda keda Wakilcin hafsoshi tara zai binciki irin rawar da sojojin suka taka ko wani abu da suka yi da ya sabawa ka'idoji da sharuddan aiki ya yin zaben da aka kammala a kasar.

Tuni dai kwamitin ya tattaro bayanai daga wadanda keda korafi don tantance sahihancin da akewa dakarun ciki har da zargin yunkurin kisan gilla ga gwamnan jihar Rivers Nyesome Wike.

Kwamitin kazalika zai binciki kashe wani Hafsa mai mukamin Laftanar da raunata karin wani Hafsa da wasu sojoji ya yin zaben Gwamna a jihar.

Gwamnan jihar Rivers Wanda Ya yi bayani ga yan kwamitin ya yi korafin irin shishshigi da sojoji a jiharsa sukai ya yin zaben al'amarin da ya bayyana ko kadan bai cancanta ba.

Masanin kimiyyar siyasa Farfesa Jibrin Ibrahim wanda ke zama wakili a cibiyar raya demokradiyya ta CDD, ya ce lalle kan bincike abune mai kyau, amma da bai kamata ace sojojinne zasu gudanar dashi ba duba da yadda suma ake zarginsu.

Ya ce kamata ya yi a sami wasu yan baruwanmu suyi binciken don tabbatar da gaskiya da kore zarge-zarge a kuma dauki matakan hana faruwar hakan nan gaba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG