Ministan Tsaron Najeriya, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar, a wata ganawa ta musamman da masu ruwa da tsaki da suka hada da sarakuna, shugabannin al'umma da na addinai da kungiyoyin mata da matasa da jami'an gwamnati, a shelkwatar rundunar soji ta uku da ke Jos a jihar Filato, ya ce matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta abu ne da za'a iya shawo kan su.
Ya ce "duk da sauki ya samu, suna son saukin ya ci gaba da samuwa yadda za’a ce kwata-kwata babu wata matsala ko kankani ta tsaro a jihar Filato."
Masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi biyar ne da suka hada da Barkin Ladi, Bokkos, Mangu, Riyom da Wase da ke fama da tashe-tashen hankula da suka hada da kai hari da ramuwar gayya, sata da lalata amfanin gona da satar dabbobi da sauran ayyukan bata gari, su ne suka halarci zaman tattaunawar.
Shugaban kungiyar Fulani ta GanAllah a jihar Filato, Garba Abdullahi Muhammad, ya ce mahalarta taron sun bayyana gaskiyar abin da ke damunsu don suna bukatar zaman lafiya.
Shi ma da yake tsokaci, Shugaban Karamar Hukumar Mangu, Emmanuel Bala Mwolpun, ya ce an fahimci juna don haka yake da yakinin samun zaman lafiya mai dorewa.
A bangaren sarakuna kuwa, basarake, Ujah Anaguta, Ponzoh Johnson Jauro Magaji ya ce idan an bai wa sarakuna matsayinsu na iyayen kasa, bisa tsarin doka, za su samu kwarin gwiwar tuhumar duk wanda ya shigo huruminsu.
Mai bai wa gwamnan jihar Filato shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Gagji Shippi mai ritaya ya jaddada muhimmancin fahimtar juna ne a yanayi irin na zamantakewa.
A cikin fiye da shekaru ashirin da aka sami rashin fahimta tsakanin wasu al'ummomin jihar Filato dai an tafka asarar rayuka da dukiyoyi masu dumbin yawa, lamarin da al’ummar ke ganin kamata ya yi a sami dawwamammen zaman lafiya.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji daga Jos:
Your browser doesn’t support HTML5